Yadda aka ceto Sheikh Ahmad Algarkawi daga hannun masu garkuwa

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa sun ceto fitaccen malamin nan sheikh Ahmad Algarkawi.

Idan dai ba a manta ba, masu garkuwa sun yi awon gaba ne da babban malamin ne a gonar sa dake Unguwar Nariya.

Bayanai dai sun nuna cewa malamin ya na rangadin gonar sa ne tare da wasu daliban sa a lokacin da aka yi garkuwa da su.

Mukhtar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sun ceto Sheikh Algarkawi da yammacin Lahadi ne, sannan a cewar sa ba a biya ko sisiba wai ko don a biya diyya ko fansa.

” A iya sani na dai ba a biya kudi ba kafin aka saki Malam.” Inji Mukhtar

Malam Ahmad Algarkawi mazaunin Unguwan Kinkinau ne dake garin Kaduna. Sannan ya na daga cikin malaman dake da dubban mabiya a garin Kaduna da kewaye.

Share.

game da Author