Jam’iyyar APC ta Kaduna ta yi watsi da dawowa da Shehu Sani jam’iyyar da hedikwatar APC ta yi.
A yau Lahadi ne Hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa ta yi fatali da dakatar da Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani da jam’iyyar tayi a Kaduna cewa bata san da haka.
Kakakin jam’iyyar APC na kasa Yekini Nabena ne ya sanar da haka a wata shimfidaddiyar takarda da ta fito daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa.
” Jam’iyyar APC ta kasa ta duba wannan wasika ta dakatar da Sanata Shehu Sani, sannan ta aika wa reshen jam’iyyar a Kaduna da ta gargadi masu yin irin wannan shiga sharo ba shanun. Sanata Shehu Sani na nan daram dan jam’iyyar APC da jam’iyyar ke alfahari da saboda haka jam’iyya ba ta san wannan magana ba na dakatar da shi ba.
” Idan ba a manta ba, sanata Shehu Sani ya ki bin a yarin masu komawa jam’iyyar PDP ne saboda kokarin sasanta wadanda ba sa ga maciji da juna a jam’iyyar.” Cewar Yekini.
Sai dai kuma jin hakan ke da wuya sai jam’iyyar a jihar Kaduna ta yi watsi da wannan matsaya ta uwar jam’iyyar.
Tace uwar jam’iyyar bata da hurumin dakatar da kowani dan jam’iyya da jihar ta dakatar ta hanyar hukunci.
Jam’iyyar tace doka ya bata dama karara ta hukunta duk wanda ya saba mata a jiha kuma tana da ikon yin haka batare da uwar jam’iyyar tayi mata katsalandan ba.
” Shehu Sani ya hada baki da Sanata Suleiman Hunkuyi suka ci mutuncin jam’iyyar a jihar Kaduna sannan suka raba kan ‘ya’yan jam’iyyar a jihar sannan kuma ace wai mazabar sa ba za su iya huntashi ba.