Dattijo Adamu Ciroma ya rasu

0

An sanar da rasuwar Adamu Ciroma daga bakin daya daga cikin iyalin mamacin, cewa ya rasu a yau Alhamis.

Ciroma wanda ya taba yin Ministan Harkokin Kudi, ya rasu a asibitin Nzamiye da ke Abuja, inda ya yi zaman jiyyar sati daya.

Ya rasu ya na da shekaru 83 a duniya.

Su ne kashinn bayan Jamhuriya ta Biyu, kuma ya taka muhimmiyar rawa a Jamhuriya ta Hudu.

Da Ciroma aka kafa jam’iyyar PDP. Za a rufe shi yau bayan an yi masa Sallah a Babban Masallacin Abuja.

A farkon tashen sa ya taba yin shugabancin kamfanin jaridar New Nigerian, a Kaduna.

Share.

game da Author