Atiku ya goyi bayan Majalisa kan kafa ‘yan sandan jihohi

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ya ba wa Majalisar Tarayya dangane da kokarin da ake yi na yi wa dokar kasa kwaskwarima da gyara ta yadda za a kafa dokar kafa ‘yan sandan jihohi.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen magance barazanar rashin tsaro a kasar nan, wanda ya ke haifar da kashe-kashen rayukan ‘yan Najeriya.

Ya kuma mika ta’aziyyar sa iyalai da abokan aikin ‘yan sandan nan bakwai da wasu mahara suka bindige a Galadimawa, Abuja.

Atiku yace ‘yan majalisar tarayya sun nuna jan hali da kishin kasa da har suka yi tunanin a yi wa dokar kasa kwaskwarima, domin a kafa ‘yan sandan jihohi a kasar nan.

Share.

game da Author