Gwamnatin jihar Cross River ta gargadi ma’aikatan asibitocin jihar cewa kowa ya shiga taitayin sa domin kuwa za ta hukunta duk ma’aikacin asibiti da aka kama yana karban kudi fiye da maralafiya ya kamata ya biya da gwamnati ta riga ta kiyasta.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Betta Edu ya bayyana haka inda ya kara da cewa gwamnati ta kuma kafa kwamiti domin ganin an bi wannan doka sau da kafa.
Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta hukunta duk wani ma’aikaci da baya zuwa aiki akan lokaci ko kuma ya ke kin zuwa.
Ya ce dole ma’aikata asibitocin jihar lallai su maida hankali wajen ganin aikin su ne kawai a gaban su ba yi wa gwamnati zagon kasa ba da jikkata marasa lafiya.