JAMB ta sake tara wa Gwamnatin Tarayya naira biliyan 7.8

0

Hukumar Shirya Jarabawar shiga Jami’a wato JAMB, ta bayyana cewa ta tara wa Gwamnatin Tarayya zunzurutun kudade har naira biliyan 7.8 a shekarar 2018.

Kakakin yada labaran JAMB Fabian Benjamin, ya tabbatar da haka a wata hirar sa da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN.

Ya ce an tara kudaden daga fam din da aka saida wa daliban da suka zauna jarabawar shiga jami’a ta 2018 wato UTME.

Sai dai kuma ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa hukumar ta JAMB tukuicin naira bilyan 2.2 daga cikin kudin domin hukumar ta yi gyare-gyaren hedikwatar ta, ta yadda za ta kasance daidai da kowace a fadin duniya.

Ya tabbatar da cewa za a kara inganta ayyukan hukumar ta yadda dalibai za su kara cin moriyar ta sosai.

A karshe ya ce a kasa da shekara biyu JAMB ta tara naira biliyan 15.6.

Share.

game da Author