‘Yan sanda sun kama mutane biyar bisa zargin buga dalolin jabu

0

Kwaminshinan ‘Yan sandan jihar Gombe, Shina Olukolu, ya tabbatar da cafke wasu mutane biyar bisa zargin laifin buga takardun kudaden jabu na dalolin Amurka.

Ya ce masu damfarar sun yi amfani da yanzu ne lokacin da ake hada-hadar tafiya aikin Hajji da niyyar su rika damfarar maniyyata.

An kama su ne da daloli guda, ‘yan dari-dari.

Kwamishinan ya kara da cewa an kama biyu daga cikin wadanda ake zargin da dala 200, bayan da suka gayyaci wani mai suna Tamin Idris daga Legas, suka ce ya je Gombe, domin ba shi canjin dala.

Daga nan sai ya gargadi maniyyata da su guji canjin dala daga mutanen da suke da shakku ko kuma wadanda suke canjin kudaden waje ba bisa ka’ida ba.

Ya ja kunnen cewa duk wanda ya shafa musu mai ga bakin cewa zai saida musu dala a arha bagas, to dan damfara ne.

Share.

game da Author