Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa, shiyyar Benin, ta bayyana cewa ta cewa ‘yan Najeriya 478 da aka yi safarar su zuwa waje a cikin watanni shida.
Kwamandan Shiyyar, Nduka Nwanwenne, ya fadi haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin Dillanci Labarai, NAN yau Talata a Benin.
Ya kara da cewa a cikin wadannan watanni shida, an kama kuma an gurfanar da masu safarar mutane har 30.
Daga nan sai ya kara da cewa an yanke wa mutane biyu hukunci, yayin da wasu 33 kuma su na fuskantar ci gaban shari’a a kotu.
Ya danganta nasarorin da hukumar ta samu a kan gudummawar da bangarori da dama suka bayar.
Sai dai kuma ya yi kukan cewa hukumar na fuskantar kalubalen yadda wasu wadanda aka yi safarar bas u fitowa su fadi wadanda suka jefa su cikin halin kuncin da suka shiga.
Ya nuna takaicin yadda wasu iyayen ke matsa wa ‘ya’yan su lambar fita waje su nemo kudi.