Shugaban ma’aikata na jihar Kebbi Abubakar Idris ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta fara biyan ma’aikatan jihar da ‘yan fansho albashin su da kudin fansho na watan Yuli tun daga ranar Litinin 16 ga wata.
Idris ya fadi haka ne ranar Litini da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi.
Idris ya kara da cewa gwamnatin ta yi haka ne domin ta karfafa wa ma’aikatan jihar guiwa da kuma su maida hankali a aikin domin ci gaban jihar.
” Idan ba a manta ba gwamnati ta yi saurin biyan albashin ma’aikatan jihar na watannin Mayu da Yuni domin ma’aikata su samu suyi hidima da shagulgulan Sallah amma wannan karon ta yi haka ne domin kula da ma’aikatan ta da kuma kara musu karfin yin aiki.
A karshe Idris ya hori ma’aikata da su yi na’am da kyawawan ayyukan da gwamnatin jihar ke yi musu sannan su kara himma don ci gaban jihar.
Discussion about this post