Yadda majalisar dokoki ta kasa ta zaftare kudaden ayyuka a kasafin kudin 2018 suka kara a nasu kason

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa majalisar kasara ta zaftare kudaden da za ayi wa mutane aiki a kasafin kudin 2018 in da sukakarkata su zuwa wasu aiyuka da wai zasu gudanar a a mazabun su.

Buhari yace majalisar ta rage kudade a fannonin kiwon lafiya, aiyukka, wutan Lantarki da gidaje da masana’antu suka kara a kudaden da za su shiga aljihun su.

Duk ayyukan da suka saka cewa za a yi, ayyuka ne da tuni gwamnati ta amince wa gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su aiwatar tuni.

1. Fannin kiwon lafiya.

A. Majalisar ta zaftare Naira miliyan 60 daga Naira miliyan 140 da aka ware domin siyo kayan aikin kula da masu cutar daji sannan da horar da ma’aikatan kiwon lafiya.

B. Ta kuma zaftare Naira miliyan 400 daga miliyan 700 din da aka ware domin siyan na’urorin kula da masu cutar daji a kasar nan.

C. Naira biliyan 2.07 da aka ware domin siyo magungunan cutar kanjamau ya koma Naira biliyan 1.1.

D. An ware Naira biliyan shida domin samar wa mutanen kasar da ingantaciyyar kiwon lafiya amma majalisar ta rage zuwa Naira biliyan 1.2

E. Naira 1.43 da aka ware domin gina gidajen sanyi da motocin sanyi da zai dauki magungunan rigakafi ya ragu zuwa miliyan 208.5.

2. Sufuri

A. Naira biliyan 7.3 da aka ware domin gina wasu manyan tituna a kasar nan sun rage su zuwa Naira biliyan 4.78

B. Majalisar ta rage Naira biliyan 1.4 daga Naira biliyan 6.9 da aka ware domin samar da wutan lantarki,ruwa da katange tashar jirgin kasa na Abraka, Oria, Oruwhorum dake Itakpe-Ajaokuta-Aladja.

C. Ta kuma rage kudin da aka ware domin gyaran tashar jiragen saman dake jihar Enugu daga Naira biliyan 2.03 zuwa Naira miliyan 530.1.

Share.

game da Author