Mutane da dama da suka soki Najeriya bayan wasan ta da Crotia sun dawo daga wannan rakiya domin kuwa Crotia da ta lallasa ta ta ragargaza Argentina da ci 3 ba ko daya a wasn dare da aka buga a kasar Rasha.
Duk da cewa akwai shahararrun ‘yan wasa kamar su Leo Messi, Aguero da sauran su abin dai bai haifar da da mai ido ba.
Yanzu dai lissafi ya cakude wa Argentina, domin Najeriya ma da aka cire wa rai za ta iya kai wa zagaye na biyu idan ta iya doke Iceland sannan kuma ta buga koda kunnen doki ne da Argentina a wasan ta na karshe,