Akalla kowane Dan majalisar Tarayya ya cusa ayyuka 13 da ya ke so a yi a mazabar sa a cikin kasafin 2018, haka Shugaba Muhammdu Buhari ya bayyana a jawabin sa bayan ya sa hannu a kasafin 2018, jiya Laraba.
Da farko da Buhari ya kai wa Majalisa kasafin naira tiriliyan 8.6 ne a ranar 7 Ga Nuwamba, 2017, amma an kara shi ya zuwa naira tiriliyan 9.1 ya zuwa cikin watan Mayu, 2018 lokacin da suka maida masa.
Buhari ya yi kukan cewa ‘yan majalisa sun yi wa kasafin 2018 kacakaca, inda kuma suka rika zaftare yawan kudaden da aka ware za a yi wasu muhimman ayyuka, yayin da suka rika cusa wasu ayyukan da ba su da muhimmanci.
Shugaba Buhari ya yi korafin cewa majalisa ta rage har naira bilyan 347 daga cikin ayyuka 4,700 da aka kebe za a yi wa jama’a.
Ya kara da cewa su kuma sun saka ayyukan da suke so a yi a mazabun su guda 6,403, na kusan naira biliyan 578.
A kan wannan ne Namdas ya ce ya kamata jama’a su kula da cewa su fa jama’a suke wakilta, don haka sun saka ayyukan da za su amfani al’ummar da suke wakilta ne kai tsaye.
YADDA MAJALISA TA CUSA AYYUKA 6, 403
Idan aka yi nazarin jawabin da Buhari ya yi, za a ga cewa akalla kowane dan majalisa ya cusa ayyuka 13 a cikin kasafin na 2018, idan har daidai-wa-daidai suka kassafa ayyukan a tsakanin su.
Za a ga cewa ‘yan majalisar tarayya su 469 ne. Sanatoci 109, su kuma mambobi 360, idan an hada 469 kenan.
Tunda an ce sun cusa ayyuka har 6,403, to kowa zai tashi da ayyuka 13 kenan idan suka raba daidai.
Wadannan ayyuka da ‘yan majalisa suka cusa, ba su daga cikin ayyukan naira bilyan 100 da ake ba su a duk shekara.
A cikin kasafin 2017, ‘yan majalisar tarayya sun yi dabara inda suka rika cusa ayyukan su a karkashin kasafin hukumomi, inda suka rika kirkiro hanyoyin yadda za a yi musu aiki da kudaden a mazabun su.
Kakakin Majalisar Tarayya, Abdulrazak Namdas, ya fitar da bayanin cewa kasafin Majalisar Tarayya ko kusa bai kai na naira bilyan 150 da ake musu ba kafin shekarar 2015.
“Kafin 2015, ana ware wa Majalisa kasafin naira biyan 150 a tsawon shekaru da dama. Amma a 2015 sai aka yanke shi ya koma naira biliyan 120. Cikin 2016 kuma sai aka kara zabtare shi ya koma naira biyan 115.
“Kasafin mu na 2017, naira bilyan 125 ne. Yanzu kuma na 2018, naira bilyan 139.5 ne. To kun ga har yanzu bai ma kai na naira bilyan 150 da ake yi masa kafin 2015 ba kenan.’’
Shugaba Buhari ya yi korafin cewa majalisa ta rage har naira bilyan 347 daga cikin ayyuka 4,700 da aka kebe za a yi wa jama’a.
Ya kara da cewa su kuma sun saka ayyukan da suke so a yi a mazabun su guda 6,403, na kusan naira bilyan 578.
Sannan kuma ya ce ’yan majalisa sun kara kasafin su daga naira bilyan 125 zuwa 139.5.
A kan wannan ne Namdas ya ce ya kamata jama’a su kula da cewa su fa jama’a suke wakilta, don haka sun saka ayyukan da za su amfani al’ummar da suke wakilta ne kai tsaye.
“Wasu ayyukan da ministoci suka cusa wa Buhari a cikin kasafin kudi, kwata-kwata ba su da wani tasiri ko muhimmancin kai tsaye ga talakawa.” Inji Mamdas.
Ita ma Majalisar Dattawa ta umarci shugabannin kwamitocin kasafin kudi da su yi nazarin kowane furuci na Shugaba Buhari, domin yin bayani dalla-dalla ga jama’ar kasar nan.
KAMAR 2017, KAMAR 2018
Zargin da Shugaba Buhari ya yi na cusa ayyuka da Majalisa ta yi a kasafin 2018, haka ma suka yi a kasafin 2017.
Lokacin da Buhari ya ke London ya na jiyya, sun yi ta gudnar da takuka tsakanin su da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo inda kiri-kiri suka nemi a cusa ayyukan su a cikin kasafin kudi.
Ranar 18 Ga July, Osinbajo ya rubuta musu wasikar cewa su cire ayyukan da suka cusa a cikin kasafin.
Sai dai kuma duk da haka, PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa akalla ayyuka 34 da majalisa ta cusa a kasafin 2017, wadanda suka kai kiyasin naira bilyan 11.5, duk Ma’aikatar Harkokin Kudade ta biya su kakaf.
Buhari dai ya kyale kasafin 2018 ne don a ci gaba a yi ayyuka, domin wuri ya kure.
Sai dai kuma a gefe daya akwai masu kallon cewa a daina ganin laifin ‘yann majalisa, domin ana yi zuki-ta-mallen makudan kudade a kwangiloli daga ofishin ministoci.
Wasu na ganin daga ofishin ministoci ana rubanya kudaden kwangiloli, kuma su ‘yan majalisa duk sun san da wannan harkalla, wasun su ma sun taba rike mukaman ministan, dalili kenan su ke bi su na zaftare kudaden a cikin kasafin kudin.
Discussion about this post