Majalisa za ta kara bincikan Abdulmumin Jibrin

0

Majalisar Tarayya ta umarci Kwamitin Ladaftarwar ta da ya binciki kalamin da Hon. Abdulmumin Jibrin ya yi a kafafen yada labarai, inda ya ce su Mambobin Majalisa Magoya bayan Buhari, ba su goyon bayan gutunguilar da wasu ke kitsawa domin a tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Dan Majalisar Tarayya Hon. Karimi Sunday ne daga jihar Kogi, ya jawo hankalin majalisar a kan kalaman da Hon. Jibrin ya yi a jiya Talata, inda suka tsame kan su da abin da Karimi ya ce wani muhimmin abu da Majaljsa ta amince a zartas, amma shi Jibrin ya fita ya na kwance wa majalisa zani a kasuwa.

Jibrin ya shiga kafafen yada labarai ne a madadin wani gungu na mambobin, ya ce masu neman a tsige Buhari fa duk gayyar ‘yan PDP ne.

Ya yi zargin cewa a lokacin da ake zaman yin tir da tsarin tafiyar mulkin Buhari, ba a ba wadanda ke goyon Bahuri damar yin magana a majalisa ba.

Kakakin Majalisa Yakubu Dogara, ya yi tir da irin rashin da’ar da Jibrin ya nuna, ya na mai cewa Jibrin sai ranar da ya ga dama ya ke zuwa majalisar, amma kuma ya fi kowa yawan hira da ‘yan jarida.

Jibrin dai bai fi wata biyu daga dawowa dakatar da aka yi masa ta sama da shekara daya.

Majalisa ta dakatar da shi ne bayan da ya fallasa cewa Dogara, mataimakin sa da sauran jiga-jigan majalisa, sun yi wa kasafin kudi na 2017 zuren ayyuka har na naira bilyan 30.

Share.

game da Author