TAMBAYA:Shin Mutumin da ya karanta kur’ani ba daidai ba, babu tajwed, ko kuma fadin harafi daidai, Yana da lada?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Bubu laifi ga mai Karatun Kur’anin da bai kware da karantun ba idan yakaranta ba Tajawidi.
Karatun Kur’ani da Tajawidi Wajibi ne ga duk wanda zai karanta shi, wanda bai kyautata karatun Kur’ani da Tajawidi ba, to, mai zunubi ne, don da Tajawidi aka saukar da shi, kuma da Tajawidi yazo garemu. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: “ dayawa mai karatun Kur’ani amma Al-Kur’anin yana tsinemasa”.
Amma wanda bai iya Tajawidi ba, kuma yana kokarin koyon karatun Al-Kur’ani, idan yakaranta Kur’ani yanada lada biyu inji Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama: Wanda yake karatun Kur’ani, amma kuma
karatun na bashi wahala kuma yana tuntube a karatun, to yanada lada lada biyu. (Bukhari da Muslim).
Dole musulmi ya koyi karatun Kur’ani kuma yakaranta gwargwadon kokarinsa. Ya kiyaye kar yabata ma’anar ayoyi, ko canza kalmomi. Ya bada himma wajin yin Tajawidi a aikace, domin shi Kur’ani da
Tajawidinsa ake karantar da shi. Duk wanda yake taka tsantsan da kokarin koyo, idan yakaranta Kur’ani batare da Tajawidi ba, a inda ya gaza to, Allah zai bashi lada ninki biyu. Kuma bai da laifi ko yayi kuskure a cikin karatun.
Ya Allah! ka saukake mana littafinka Al-Kur’ani kuma kasa ya cecemu. Amin
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali
Harkatul Falahil- Islam
Barnawa Kaduna.