Ali Nuhu da wasu ‘yan Kannywood sun ziyarci Saraki

0

A yau Laraba ne fitaccen dan wasan fina-finan Kannywood Ali Nuhu da wasu ‘yan wasan Kannywood suka ziyarci shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki a ofishin sa.

Saraki ya dauki hotuna da jaruman sannan ya jinjina musu kan irin namijin kakarin da suke yi a sana’ar su na shirya fina-finai.

” Yaba muku ya zama dole sannan kuma ayi muku jinjina kan yadda kuka mai da hankali wajen bunkasa wannan sana’a da ganin karbuwar sa ga miliyoyin mutane da sannan samar da aikin yi da masana’antar ta yi wa matasa da dama.” Inji Saraki.

Share.

game da Author