Dariye zai yi zaman gidan yari na tsawon shekara 14 – Hukuncin Kotu

0

Kwanaki kadan bayan kotu ta daure tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame, Shima tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye na kan gabar haka domin kotu ta tabbatar da kama shi da laifin handame kudin jihar da yakai naira biyan 1.161.

An kama Dariye da laifin saka wasu daga cikin kudaden a asusun jam’iyyar PDP a wancan lokaci, sannan kuma da loda wasu a asusun wasu kamfanonin boge.

Alkalin Kotun, Adebukola Banjoko, ta ce duk da kin amsa laifi da Dariye yayi, an tabbatar da hannun sa dumu-dumu cikin harkallar kudaden.

Bayan kusan awa 5 da akayi na zaman kotun da take yanke hukunci, Alkalin Kotun Banjoko ta daure Sanata Joshua Dariye har na tsawon shekaru 14 a gidan yari sannan ba ta bashi damar neman beli ba.

Alkali Banjoko ta ce kotu ta kama Dariya da laifin cin amanar jihar sa da handame kudin jihar.

Share.

game da Author