Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Adamawa ya rasu a Umra

0

Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla ya rasu.

Da yawan makusantar siyasar Jibrilla, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa shugaban na ma’aiktan ya rasu da asubahin yau Litinin.

Ya rasu a Saudiyya, inda ya je domin yin Umra.

Kokarin da Premium Times ta yi domin jin ta bakin Kwamishinan Yada Labaran Jihar Adamawa, Ahmed Sajo ya ci tura, domin a ji abin da gwamnati za ta ce.

Share.

game da Author