2019: Makarfi ya fito takarar shugaban kasa ka’in-da-na’in

0

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya bayyna cewa shi ma ya fito takarar neman kujerar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP.

Makarfi wanda shi ne ya sauka daga shugabancin riko na jam’iyyar PDP, kafin hawan shugaban jam’iyyar na yanzu, Uche Secondus, ya bayyana wannan aniya tasa a wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a gidan sa da ke Kaduna, a ranar Lahadi.

Ya jaddada cewa kafin ya yanke tunanin tsayawa ko ayyana fitowa takarar, sai da ya tuntubi jama’a da dama a fadin kasar nan.

Sai dai kuma inji shi, wannan ba wai ya na nufin shi ne dan takarar da jam’iyyar gaba daya ta amince da shi ba.

Ya kara da cewa ya kara fahimtar halin da Najeriya ke ciki, ta hanyar yawon tuntubar jama’a da ya yi domin neman shawarar su ta batun tsayawar sa ta kara.

“Ina da gogewar da zan iya mulkin Najeriya, kuma bakin gwargwado na san mulki. Na yi aikin banki, nayi kwamishinan harkokin kudi da tsare-tsare na jihar Kaduna, sannan kuma na yi gwamnan jihar Kaduna tsawon shekaru takwas.”

“Sannan kuma na kwashi garabasar sanin yadda ake tafiyar da shugabanci na jam’iyya a lokacin da shugabancin jam’iyyar PDP ya fado a hannu na.”

“To idan ba za ka iya tafiyar da shugabancin jam’iyya kamar PDP ba, zai yi wuya ka iya tafiyar da mulki. Haka duk wanda ya shugabanci jihar Kaduna, wadda kowa ya san ta da kwatagwangwamar matsaloli, har ya shawo kan su, to zai iya shugabancin Najeriya.

Makarfi ya kara da cewa a yadda ya yi shugabancin jihar Kaduna, yadda ya samu jihar cikin munanan rikice-rikice, da kuma yadda ya shawo kan matsalolin aka samu wanzuwar zaman lafiya, don haka ya ce batun matsalar tsaro a kasar nan, da kuma hanyoyin shawo kan su duk ba za su gagare shi ba.

Makarfi zai fafata da irin su tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido.

Share.

game da Author