Akwai yiwuwar an sake coge da kare-kare a kasafin Kudin 2018 – Jibrin

0

Dan majalisa dake wakiltar Bebeji/Kiru a majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin ya yi wata yar gajeruwar tsokaci cewa, zai dan yi bayanai kan da kasafin kudin 2018 da majalisar wakilai ta amince da shi yau, Litinin.

Jibrin ya bayyana haka ne a shafin sa na tiwita, inda ya ce zai tattauna da mabiyan sa sannan zai masa tambayoyi a wannan hira da zai yi.

An dai ga Abdulmumini a gaban kakakin majalisar Yakubu Dogara, suna tattaunawa kan wasu batutuwa da kamar shi bai gamsu da su ba a kasafin kudin 2018 din.

Idan ba a manta ba majalisar wakilai ta dakatar da jibrin na sama da shekara daya a dalilin badakalar coge a kasafin kudin 2016 inda ya zargi wasu shugabannin majalisar da yin aringizo a kasafin kudin a wancan lokaci.

Share.

game da Author