Wata Kotun Majistare a Kano ta tsare wata amarya a bisa zargin ta sa wa mijin ta maganin bera, wato samandagari a abinci ya ci mutu.
Amaryar dai an tsare ta ne a gidan adana kangararrun yara, kasancewa karamar yarinya ce mai shekaru 16 kacal.
Ana tuhumar amaryar ‘yar kauyen Shittar cikin Karamar Hukumar Danbatta a Jihar Kano da laifin kisa.
Zan zarge ta da zuba wa mijin ta Auwal Isa guba a abinci ya ci ya mutu.
Mai Shari’a Fatima Adamu, ta daga karar zuwa 7 Ga Yuni, 2018.
Mai gabatar da kara ya ce wani mai suna Ibrahim Yahaya ne ya kawo rahoton faruwar al’amarin a ofishin ‘yan sanda na Danbatta.
Mai gabatar da kara Aluta Mijinyawa, ya shaida wa kotun cewa amaryar ta dafa abinci a ranar 22 Ga Afrilu, 2018, ta zuba gubar a cikin abincin angon na ta.
“Bayan mijin ya ci abincin ne ya mutu a nan take.” Inji Mijinyawa.
Sai dai kuma wadda ake tuhuma din ta ce ba ita ce ta kashe shi ba.