Rundunar ‘yan sanda ta gabatar wa manema labarai da wasu da ta ke zargi da safarar makamai, kashe-kashe da kuma tuhumar da laifukan da su ka hada garkuwa da mutane.
Kakakin Rundunar ‘yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ya lissafa sunayen wadanda aka kama din da kuma makaman da aka samu a hannun su.
An gabatar da su ne a gaban manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai, bayan da zaratan ‘yan sanda da aka tura jihohin biyu, a karkashin Abba Kyari su ka yi nasarar zakulon su.
Wannan dai wani sabon yunkuri ne da zaratan jami’an tsaro na musamman da Sufeto Janar na ‘Yan sanda ya kafa suka yi.
An kama Mbashe, wani dan kauyen Mbajima da ke karkashin karamar hukumar Katsina-Aa ya na jigilar makamai da harsasai ga masu kashe mutane da kuma masunyinngarkuwq da su.
Shi ne da kan sa ya ce ya rika kai wa dan ta’adda Terwase Akwaza muggan makamai.
Akwai kuma kabiru Idris, Miracle Emmanuel, da Husseini Safiyanu, wadanda aka kama a jihar Taraba da bindigogi 5 kirar AK47, jigidar harsasai 8. Su ma sun ce masu kisan mutane suke yi wa dillancin muggan makamai a cikin kauyukan Benuwai da Taraba.
An kuma gabatar da wasu rikakkun masu garkuwa da mutane da suka addabi jama’a da sacewa a jihohin Benuwai, Taraba da Nasarawa.
Wasu rikakkun dillalan muggan makamai da aka gabatar kuma sun hada da:
1. Emmanuel Ushehemba Kwembe
2. Sekad Uver
3. Ordure Fada
4. Stephen Jirgba
5. Peter Lorham
6. Achir Gabriel
7. Lorhemen Akwambe
Dukkanin su kuma kabilun jihar Benuwai ne, sannan an kama makamai daban-daban a hannun su.
Discussion about this post