‘Yan sanda sun fara gungunin yanke musu albashi

0

Wasu jami’an ‘yan sanda sun nuna takaicin yadda ake yanke musu albashin su a tsawon watanni da dama, su na cewa abin fa ya kara jefa su cikin kuncin rayuwa.

Jamai’an ‘yan sanda da dama a fadin kasar nan su na ta gungunin cewa ana yanke musu albashi, musamman ma albashin watan Fabrairu, Maris da na Afrilu.

Wadanda su ka yarda aka yi hira da su, amma su ka roki kada a ambaci sunayen su, sunn bayyana cewa sun yi iyakar kokarin su nemi sanin dalilin zaftare musu hakkin su, amma abin ya gagara.

PREMIUM TIMES ta gano yadda dandazon masu korafin ke ta zarya zuwa ofisoshin Akanta Janar na Tarayya da kuma Babbar Hedikwatar Rundunar ‘Yan sanda a Abuja domin bin ba’asin kudaden su.

Wani Saje ya shaida cewa tun da wannan shekarar ta kama, a duk wata ana cizge masa naira N15,000, kuma hakan ya haifar masa tawaya sosai wajen daukar dawainiyar ciyar da iyalin sa. Kuma ya ce duk da korafin da ya ke yawan kaiwa, ba a daina cire masa kudin a duk karshen wata ba.

Ita ma wata Sufeto mace, wadda ke Hedikwatar ‘Yan sanda ta Legas, ta ce ta zo har Abuja ta kawo kukan cewa watanni da dama kenan a duk wata ana zabtare mata N27,000, kuma har yau ba daina ba, kuma ba a yi mata bayani ba.

“Ba fa ni kadai abin ya shafa ba. Na san kamar wasu kananan ‘yan sanda 30 wadanda albashin su bai wuce naira 40,000 a wata ba, amma ana cire musu naira N15,000 duk wata. Akwai kuma manyan jami’ai masu karbar N100,000 a wata, amma ana cire musu N40,000 zuwa N50,000 duk wata.” Inji ta.

Wata jami’ar ‘yar sanda da aka tambaya kuwa, ta ce abin bai shafe ta ba, amma dai ta san wasu Sufetoci biyar da abin ya shafa, kuma cikin halin damuwa sosai.

“Ai ba ka ma san ‘yan sanda na cikin garari ba, sai ka je ofishin Akanta Janar na Tarayya, za ka ga yadda cincirindon masu korafi ke cika ofishin a kullum, amma hakan bai haka idan wani watan ya zo a sake cire musu kudaden ba.”

Da dama daga cikin wasu kuma su na korafin rashin biyan albashi da wuri, har sai sabon wata ya shiga da kwana 10 zuwa 15.

Kakakin Rundunar ‘Yan sanda ta kasa, Jimoh Moshood ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da matsalar jinkirin albashin, amma ya ce ana ta kokarin gyara inda tangar ta ke.

Ya kuma roki wadanda aka cire wa kudi daga albashin Janairu har zuwa Afrilu da su kara hakuri, za a shawo kan matsalar da gaggawa.

Shi kuwa ofishin Akanta Janar ya tabbatar da cewa matsalar kwamfuta ce aka samu, amma ba da gangan ba ne.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Fabrairu, zakakurin dan sanda mai kamo ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, Abba Kyari, ya shiga shafin sa na soshiyal midiya inda ya yi korafi kan rashin bai wa jami’an ‘yan sanda masu saida ran su isasshen kudin da ya kamata su gudanar da aikin su.

Ya ce abin da ake bayarwa bai wuce kashi 20 bisa 100 na abin da ya kamata a ba su ba.

Share.

game da Author