Majalisar Dattawa ta gayyaci Emiefile, Adeosun da Dan-Ali a kan Dala miliyan 462

0

Majalisar Dattawa ta nemi Gwamnan Babban Bankin Tarayya, Godwin Emiefile, Ministar Kudi Kemi Adeosun da na Tsaro Mansir Dan-Ali su bayyana domin su yi bayanin yadda aka kamfaci dala miliyan 462 daga asusun Gwamnatin Tarayya ba tare da amincewar Majalisar ba.

Sanatan da ke shugabantar Kwamitin Tantancewa da Bin Ka’idoji ne, Sam Anyawu ya kawo kudirin neman a gayyace su din, kuma zauren majalisar ya amince da haka.

Anyawu ya buga misali ne da sashe na 80 na dokar Najeriya, inda dokar ta haramta wa ko ma wane ya ciri kudi daga Asusun Gwamnatin Tarayya, ba tare da sani da amincewar Majalisa ba.

A kan haka ne sai Anyawu ya bukace a kira ministocin biyu tare da gwamnan babban bankin tarayya, domin su bayyana a gaban kwamitin kasafin kudi, su yi bayanin yadda aka ciri kudin da kuma abin da aka yi da su.

Ya ce an cire kudin amma kuma shi dai a iya sanin sa, ba a taba kawo batun neman iznin a ciri kudin a majalisar dattawa ba.

Share.

game da Author