Gwamnati za ta mai da hankali wajen ceto masu fama da cutar dakushewar kwakwalwa

0

Gwamnatin tarayya za ta maida hankali wajen zuba kudade masu yawa domin samar wa masu fama da cutar dake yin lahani ga kwakwalwa ‘Neurological development Disorder’ kula a Najeriya.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta yi wa masu fama da cutar tanaji domin samar musu da kular da ya kamata.

Minista Adewole ya bayyana haka ne a Abuja a taron kaddamar da littafin da wani marubuci Austin Amaechi ya rubuta kan masu fama da irin wannan cuta mai taken ‘Enhancing Everyday Life – Non-Existent Therapeutic Services in Nigeria, let’s do something about it’.

Bayanai sun nuna cewa cutar dake illata kwakwalwa ‘Neurological development Disorder’ cuta ce dakan kama mutum tun yana yaro, wato daga haihuwa zuwa shekara 3.

Cutar kan sa yaro samun jinkiri wajen sadar da sako a kwakwalwar sa da hana shi iya yin mu’amula da ‘yan uwan sa.

Adewole ya ce gwamnati za ta iya samar wa irin wadannan mutane dake fama da wannan cuta kulan da ya kamace su ta hanyar maida hankali wajen wadatar da asibitoci kwararrun likitoci domin taimaka musu.

Bayan haka marubucin littafin Amaechi ya fadi dalilan da ya sa ya rubuta wannan littafi cewa yayi haka ne domin wayar wa mutane kai game cutar, wahalar da iyayen ‘ya’yan kan shiga da hanyoyin da ya kamata a kula da irin wadannan yara.

” Cutar ta dade a duniya sai dai mafi yawan mutane basu da masaniya ne a kan sa sannan wadanda suka san cutar ba su da sanin yadda ya kamata su yi jinyar masu dauke da cutar.”

Share.

game da Author