Kungiyar ‘yan takarar Kansiloli na jam’iyyar APC a jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar lumana ranar Laraba don nuna fushin su da rashin amincewar su ga sakamakon zaben fidda da ‘yan takara na jam’iyyar da akayi makonni biyu da suka wuce.
Shugaban kungiyar Aminu Adamu ya bayyana wa sauran ‘yan takaran da manema labarai cewa abinda akayi ranar zaben ba zabe bane kawai nuna wanda ake so kawai aka zo aka fadi wa sauran ‘yan takara.
” Alkawarin da gwamna El-Rufai yayi cewa gwamnati ko jami’an gwamnati ba za su sa ka baki ko hannu a zaben ba ne ya sa muka fito domin yin takarar kujerun kansila a gundumomin mu amma sai gashi wasu jami’an gwamnati sun zo sun dagula abin inda suka zabi nasu ba tare da an gudanar da zaben fidda dan takarar ba.
” Mun rubuta wa gwamnatin jihar domin ta dauki mataki kan haka amma shiru kake ji kamar an ci shirwa. Dalilin da ya sa ke nan muka fito wannan zanga-zanga da kuma bayyana wa gwamnati cewa akwai matsalar gaske idan fa jam’iyyar APC ta ce ta haka zata yi abubuwan ta.
Sakataren jam’iyyar Yahaya Pate ya karyata wannan korafi, inda ya ce babu wani abu kamar haka da ya faru a kananan a zaben fidda dan takara na jam’iyyar.