BIDIYO: Kalli yadda Soja ya lakada wa wani direba dukan tsiya don ya ki bashi cin hancin naira 20

0

Wani direban motar daukar fasinjoji mallakar jihar Filato, ya sha maka kawai don yaki ya ba wani soja da ya tare motar su a a hanyar Filato zuwa Abuja nai 20.

Wani Fasinja dake cikin motar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sojan ya tsayar da motar su ne in da bayan haka ya nemi direban ya bashi cin hancin naira 20.

” Kin haka da direban yayi sai ya bukace shi da ya bude bayan motar sa ya fiddo duka kayan dake ciki. Duk da haka, hakan bai ishi sojan ba sai ko ya hau mauje direban yana faffala masa mari.

Mutane daga cikin motan ne suka yi ta rokon sojan kafin nan Allah ya sa ya hakura.

Kalli Bidiyo

Share.

game da Author