BADAKALAR NAIRA BILIYAN 10: Yadda ‘Yan Majalisar Tarayya suka raba sauran canjin naira biliyan 3.4

0

Tsakanin makon da ya gabata zuwa farkon wannan makon, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku labarin yadda Ministar Kudi, Kemi Adeosun, Saraki, Dogara da Akanta Janar suka yi wa naira bilyan goma rabon-tuwon-gayya.

Mun kuma kawo muku dalla-dallar yadda aka balla-bushasha da naira biliyan shida a cikin kudin, inda har Saraki da Dogara suka yi barazana da borin-kunyar kai jaridar kotu.

A yau kuma ga mu dauke da ci gaban labarin, mai nuna yadda aka yi wa cikon canjin naira biliyan 3.4 watanda da rana-tsaka.

Yawanci an kamfaci kudaden ne ta hanyar yi wa kwangila daya biya sau biyu. Misali, Majalisar Dattawa ta biya kamfanin Messrs Quantita Services Limited naira milyan 115, alhali kuma a baya an biya kamfanin wata naira milyan 100 ta hanyar bad-da-bami da bad-da-kamar sunan aikin da aka yi.

An ba kamfanin Alik-Dove Services naira milyan 100 ladar aikin gyaran fitilun kan titin cikin majalisar tarayya. Alhali kuma shi ma kamfanin Quantita an ba shi naira milyan 50 a kwangilar aikin gyaran fitilun kan titin.

Duk yawanci an cire wadannan makudan kudade ne da sunan an sayo kayan ofis, gyaran ofisoshi, kula da su da kuma dakunan taro, kamar yadda takardar bayanan yadda aka yi watandar kudaden ta nuna.

An bayar da kwangilar naira milyan 33,918,750 ga kamfanin Popoona Star. Bayan an cire kudin, sai kuma aka kara cire wannan adadin kudin da sunan kwangilar wancan aikin ga kamfanin Yujam Nigeria Limited.

Sama da kamfanoni 25 ne aka yi amfani da su aka rika karkatar da wuri-na-gugar-wuri har naira bilyan 3.4.

An kuma bayar da kwangilolin naira miliyan 47, miliyan 100, miliyan 38, miliyan 55.5 da kuma miliyan 100 ga wasu kamfanoni daban-daban, wadanda babu takamaimen aikin da suka yi, ko kuma babu kayan da suka sayo domin a gani a tantance.

Baya ga wata naira miliyan 454 da aka kashe wajen sayen kayan ofis, an kuma kashe wata naira miliyan 100 wadda aka ba kamfanin Navadee Integrated domin kawo kayan aikin ofis.

Share.

game da Author