Kakakin Majalisa ya rasu

0

An bayyana rasuwar Kakakin majalisar jihar Oyo, Micheal Adeyemo. Daya daga cikin mambobin majalisar ne ya shaida wa PREMIUM TIMES mutuwar, sai dai bai fadi sanadiyyar ajalin na sa ba.

Ya zuwa yanzu dai an garzaya da gawar mamacin a dakin adana gawa.

Idan ba a manta ba, farkon wannan watan PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton mutuwar ‘yan majalisa tara tsakanin sanatoci, mambobin tarayya da kuma na jihohi.

Wadannan ‘yan majalisa har da na cikon goma din, duk sun mutu ne tsakanin 2015 bayan kama mulkin wannan gwamnati zuwa yau.

Kakakin majalisar Oyo Ya rasu ya na da shekaru 47.

Share.

game da Author