A ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gina barikin soji a garin Mubu dake jihar Adamawa.
Mohammed Monguno wanda ke wakiltan jihar Barno daga jami’yyan APC ya jagoranci wannan mahawara a zauren majalisar inda ya bayyana cewa Mubi gari ce da ta zama dandalin ‘yan kasuwa a wannan yankin sannan ta yi iyaka da kauyukan Michika, Uba da Hong.
Ya ce Mubi, Uba, Michika da Hong garuruwa ne dake kusa da babbar mabuyar Boko Haram (dajin Sambisa) amma haka wadannan wurare suke batare da barikin soja ba.
Ya ce barikin soja dake kusa da su shine wadanda suke Yola da Biu kuma suna da nisan kilomita 300.
” Kamata ya yi a samar wa wadannan wurare kariya ta hanyar gina musu barikin soja ko dan saboda yadda suke kusa da dajin Sambisa.”
Daga karshe kakakin majalisar Yakubu Dogara ya dankawa kwamitin soji domin duba wannan batu.