Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa tsananin riko da igiyar yin adalci da ta yi ne ya sa ta soki maigidan nata a baya, har ta ce ba za ta mara masa baya ta fita ta na yi masa kamfen domin ya sake cin zabe a karo na biyu ba.
Ta bayyana cewa hakan da ta yi ba wai rashin biyayya ce ko kuma yin fito-na-fito da mijin na ta kuma shugaban kasar nan a fili ba.
Aisha Buhari ta yi wannan bayani ne a cikin wata wasika da ta aika wa Gidan Jaridar Vanguard, wadda ta zabi Uwargidan Shugaba Buhari a Matsayin Gwarzon Shekarar 2017 na jaridar.
Aisha ta ja hankalin duniya kakaf a cikin 2017 a watan Oktoba, inda a cikin wata hira da Sashen Hausa na BBC ta bayyana cewa ta na fargabar cewa wannan gwamnatin ta kauce daga alkiblar dalilan da suka sa aka zabe ta.
A lokacin Aisha ta ce muddun aka ci gaba da tafiya a haka, to ita fa ba za ta fito kamar yadda ta yi a zaben 2015 ba, inda ta rika fita ta na taya mijin nata yakin neman zabe. Ta ce idan mijn na ta bai canja takun gwamnati ba, to a 2019 ba za a yi kamfen da ita ba.
Wannan furucin da ta yi ne shi kuma Buharin da kan sa ya maida ma ta martani a wani taro a kasar waje a lokacin da ya ke amsa wata tambaya, ya na cewa, ta hutar da kan ta, ta tsaya matsayin ta a aikin dafa abinci da kuma daya aikin na ta na zaman aure a dakin su na kwana.
Wannan habaici da Buhari ya yi wa matar sa, ya janyo masa maganganu da gulmace-gulmace da kuma habaice-habaice daga jama’a, musamman ‘yan adawa.
Tun bayan da Aisha ta yi wancan kalami kusan shekaru biyu, har yau Buhari bai canja ministoci ko yin sauye-sauyen ministocin ba, duk kuwa da cewa a cikin makon da ya gabata ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara a 2019.
A cikin wasikar godiya da kuma karbar kyautar Gwarzuwar Shekara da Vanguard ta bai wa Aisha, ba ta bayyana cewa za ta goyi bayan mijin na ta ko ba za ta goyi baya ba.