MAULIDIN NYASS: Kowa ya yanki rajistar zabe -Dahiru Bauchi

0

A wani kasaitaccen gangamin taron maulidin zagayowar ranar haihuwar Sheikh Ibrahim Nyass, da aka gudanar a Babban Birnin Tarayya Abuja, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi kakkausan kira ga mabiya Darikar Tijjaniya da su gaggauta yankar rajistar zaben 2019, domin ta haka ne kawai za su kori wanda ba su so daga mulki, kuma zu zabi wanda ko wadanda su ke so.

Da ya ke jawabi a taron maulidin karo na 32, Dahiru Bauchi ya ce katin rajistar zabe ne kadai babban makamin da talaka zai yi amfani da shi domin ya huce haushin zaben shugabanni.

Taron wanda mabiya Darikar Tijjaniya suka shirya, ya samu halartar dimbin jama’ar da ake kyautata zaton cewa ba a taba yin taron da ya kai shi yawan maja’a a Abuja ba, imma a cikin taron siyasa ko na addini ko na wasu shagulgula.

Ya kuma yi rokon cewa su tabbatar sun zabi mutane masu inganci da cancantar da suka san su na da kyakkyawan abin tunawa wanda su ka yi wa al’umma a baya kuma ra’ayin su ya zo daidai da abin da talakawa ke bukata.

Ya kara da c ewa makasudin wannan Maulidi shi ne domin a yi bukin tunawa da gagarimin aikin dabbaka addinin musulunci da Sheikh Ibrahim Nyass ya yi a Afrika.

Ya ce Nyass ya bayar da gagarimar ci gaba wajen yada addinin musulunci a Afrka da ma duniya baki daya.

Ya kuma kara da cewa an gudanar da taron domin a yi addu’a Allah ya magance matsalar rashin tsaro ya kawo zaman lafiya da walwala a kasar nan.

Bauchi ya ce a irin halin da kasar nan ke ciki, to duk wani abu da za a yi domin magance hakan fiye da addu’a.

Da ya ke jawabi tun da farko, Shugaba Muhammadu Buhari wanda Ministan Ilmi Adamu Adamau ya wakilta, ya jinjina wa Darikar Tijjaniyya saboda gudummawar da ta bayar wajen fadada alddinin musulunci.

Ya ce gwamnatin sa za ta mara wa mabiya darikar baya wajen addu’ar zaman lafiya. Ya kuma nemi su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a.

ABUJA TA YI CIKAR DA BA TA TABA YI BA

Tun a ranar Juma’a da safiya Babban Birni Tarayya Abuja ya fara cika da baki mahalarta taron Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass. Daga ko ina cikin Najeriya da wasu kasashen da ke makwautaka da Najeriya, jama’a musamman matasa da manyan magidanda sun rika tururuwar shiga cikin Abuja. Wasu a kan manyan motocin roka, kanta da tirela, wasu kuma a kan bas-bas da kananan motocin haya da suka hada da Sharon, Vectra da Golf. Da dama kuma masu ababen hawa na su na kan su, sun zo da motocin su daga sassan kasar nan daban daban.

Ko ta ina aka duba a cikin Abuja, motocin baki ne mahalarta taro a kan titi da gefen titi. Wasu motocin dauke da jama’a su na neman wurin yada zango, wasu kuma an rigaya an sauke fasinjoji.

Duk ta inda ka duba gefen titi kuma jama’a ne hululu, wasu zaune, wasu na tafiya, wasu kuma na yawon zagayawa kallon gari.

Ya zuwa yammacin Juma;a kuwa, yankin Central Area na Abuja ya gagara shiguwa saboda cinkoson jama’a da ababen hawa, tun daga bangaren babban masallacin juma’a ana Abuja har zuwa Eagle Square, duk babu masaka tsinke.

Kusan rabi birnin Abuja ya hargitse da cinkoson motoci da kuma tirmitsitsin jama’a a Wuse 11 da Centaral Area, ta yadda masu ababen hawa sun rika kaucewa su na yin dogon zagaye su nemi mafita.

Ko ta in aka duba a jikin motocin mahalarta maulidi, fasta ce mai dauke da hoton Sheikh Ibarahim Nyass da Sheikh Dahiru Bauchi.

JUMA’A DA DARE

Abuja ta sake cushewa da dimbin baki mahalarta can cikin dare a ranar Juma’a, kasancewa washegari Asabar ne za a gudanar da taron. Da wuya ka ga titin da babu motocin baki ko dandazon masu halartar taron maulidin ba.

Dubban jama’a sun kwana kan titina har gari ya waye. Yayin da a Central Area kuwa dubban mahalartan da suka kwana kan fiti da gefen titina su ka rika zankada zikiri, wasu kuma suka rika daura alwala su ka kashe dare su na nafilfili.

YADDA MASU ABINCI SU KA YI CINIKI

Tun daga yammacin Juma’a har washegari Asabar, Abuja ta gamu da gamon ta, domin ba a taba ganin tulin bolar kwanukan sayar da abincin-tafi-da-gidan ka ba, wato ‘takeaway’ kamar lokacin bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Nyas.

Du wani abin da za ka je nema a kasuwa na masarufi ko sutura ko kayan marmari da abincin sayarwa duk an baje-kolin sa a wurin taron maulidin.

Duk inda ka duba robobin abinci ne da kuma ledojin ‘pure water.’ Tun daga Masallacin Central Area har filin taro, banda ledoji da takardun da aka ci tsire, balangu da abinci da ruwa da gwangwanayen madara da lemun gwamgwani da na roba ba ka ganin komai.

SIYASA A TARON MAULIDIN

Duk da cewa taro ne na maulidi, amma siyasa ta shigo ganin yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya yi kira da kowane mabiyain Tijjaniyya ya tashi ya yanki rajistar shirya wa zaben 2019.

Idan ba a manta ba, Dahiru Bauchi ya sha bayyana ra’ayin sa dangane da zabe da kuma irin mutanen da ya kamata a zaba.

YADDA KWANKWASIYYA TA KWACE WA BUHARIYYA TARON MAULIDI

Kallo ya koma sama, a lokacin da Sanata Rabi’u Kwankwaso da dandazon jama’ar sa suka bayyana a wurin taron Maulidi a filin Eagle Square.

Kwankwaso wanda yayi shigar sa ta al’ada, wato fararen kaya da jar hula, ya sha wahala kwarai saboda cincirindon jama’a da suka kwaye motar su na kururuta shi. Wasu na “Sai dan Musa”, wasu sa “Sai ka yi”, wasu kuma na tsalle su na “Daga dan Daura sai dan Musa.” Matasa ’yan baberiya kuma sai tsalle su ke su na, “Madugu ja mu ka kai mu, ko dare ko rana.” Akwai masu cewa, “Sai ka yi ko ba jam’iyya!”

Shigar Kwankwaso wurin ya haifar da ra’ayoyi da dama. Wasu na ganin kamar taron ya nemi ya koma na Kwankwasiyya, wasu kuma na ganin cewa Kwankwaso ya yi amfani da damar taron ya ci kasuwa la’ada waje.

A soshiyal midiya kuma tuni wasu magoya bayan Buhariyya suka fara sukar dalilin zuwan Kwankwaso a wurin.

Sai dai kuma Usman Garba, wani da ya bayyana wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa daga Karamar Hukumar Faskari ta jihar Katsina ya je taron maulidin, ya ce rashin sani ne kawai da kuma jahilcin wasu har suke sukar Kwankwaso don ya je taron Mauidi.

“Me ya sa lokacin da Buhari ke shiga coci-coci ba su soke shi ba, wasun su ma gani suke yi kamar aikin ibada ko aikin lada ya je yi a coci?” Inji Garba.

FASTAR KWANKWASO TA CIKA ABUJA

Tun daga Zone 4 bangaren da ‘yan canjin kudaden kasashen waje su ka yi kaka-gida, da bangaren sama da karkashin gadar Wuse Market da Central Arewa, duk inda ka duba fastar Kwankwaso ce an hada hoton sa tare da hoton Sheikh Ibrahim Nyass.

Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan Kwankwaso ya kusa taron Abuja, daga baya ya fice inda ya garzaya ya halarci wani taron na Maulidi a garin Kaduna.

A taron Kaduna dai Janar Abdulrahman Dambazau ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari.

TARO YA WATSE, AN BAR ABUJA DA TULIN SHARA

Har zuwa ranar Lahadi da rana akwai tulin shara a kan titina da kuma gefen titinan musamman inda mahalarta taron suka fi yin kaka-gida.

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA da ya azagaya a yau Lahadi, ya ga masu shara su na ta gaganiyar sharar titina awasuyankunan birnin.

Sai dai kuma daidai lokacin da ya kewayo daidai kofar shiga Otal din Sheraton, gaba daya bakin shiga otal din biji-biji yake da ledoji da roboin cin abinci da kwalayen lemu.

Masu sayar da abinci da kayan masarufi da na marmari da PREMIUM TIMES HAUSA ta zanta da su, da yawan su ra’ayin su daya da Nasiru mai saida ‘pure water.’

“Mu Allah ya kai mu taron Maulidi na shekara mai zuwa, kuma Allah ya sa a maimaita a Abuja. Domin tun da na ke ban taba yin ciniki kamar na wannan ranar ba.

“Kai ni fa gobe kwaniya ta zan yi ba zan fita talla ba, dama gobe Lahadi idan ma na fita ba ciniki zan yi a cikin kasuwa ba, tunda yawanci ba a fitowa.”

Share.

game da Author