Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Terna Tyopev ya sanar da rasuwar mutane uku sanadiyyar harin da aka kai a kauyen Dong dake karamar hukumar Jos ta kudu.
A bayanan da ya yi wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho ranar Juma’a Tyopev ya ce wasu mahara ne suka kai hari kauyen dong a daren Alhamis inda mutane uku suka rasa rayukan su.
Bayan haka limamin cocin darikan katolika a kauyen Anthony Opara ya tabbatar da wannan hari sannan ya ce yanzu haka suna shirin bizine wadanda suka rasu ne.
Ya ce an kona gidaje sama da 15, sannan wasu sun bace.
” Wannan shine hari na biyu da ake kawo wannan kauye a jere cikin makonni biyu da suka wuce. Sannan har yanzu muna neman wadanda suka bace.”