Gidauniyar ESLF ta tallafa wa marasa karfi 20,000

0

Gidauniyar uwar gidan gwamnan jihar Benuwai Eunice Ortom ‘Eunice Spring of Life Foundation (ESLF)’ ta tallafa wa marasa karfi 20,000 da hanyoyin samun Kiwon lafiya mai nagarta.

Shugaban gidauniyar kuma matar gwamnan jihar Eunice Ortom ta sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis a taron tallafa tallakawa da ingantaciyar kiwon lafiya karo na uku da gidauniyar ta fara a Utonkon.

Gidauniyar za ta kula da mutanen dake fama da cututtukan da suka hada da zazzabin cizon sauro,amai da gudawa da zazzabin ‘Typhoid’ a duk mazabun jihar.

Eunice ta ce gidauniyar za ta bunkasa cibiyar kiwon lafiyar dake Ikpomolokpo da kayan aikin yin fida sannan za ta raba wa asibitocin da suka fi bukata gudunmawar gadajen kwanciya 10 wanda asibiti mai zaman kanta ‘Echo Scan Services Limited’ a Abuja ta bada.

A karshe jami’ar gidauniyar Tine Agernor ta ce cikin shirye shiryen tallafi da gidauniyyar ta shirya sun hada da bunkasa fannoni uku a jihar wanda suka hada da kiwon lafiya, ilimi da tallafa wa masu kananan sana’o’i.

Share.

game da Author