Cutar zazzabin Lassa ta sake bullowa a Abuja

0

Shugaban fannin kiwon lafiya na sakatariyan birin taraya FCT Humphrey Okoroukwu ya sanar da cewa cutar Lassa ta sake bullowa a jihar.

Okoroukwu ya sanar da hakan ne wa kamfanin dillancin labaran Najeriya ranara Juma’a inda ya bayyana cewa sun gano haka ne ranar Laraba a jikin wani mutumi wanda bayan an kawo shi asibitin ne likitoci suka gano sannan suka bashi magani.

Ya ce a yanzu haka mara lafiyan ya fara samun sauki bayan kula da ya samu.

” Muna da tabbacin cewa mutane uku sun kamu da cutar zazzabin Lassa tsakanin watani uku da suka wuce, daya daga cikin su ya rasu tun a watan Janairu.”

Okorouko ya gargadi mutane da su kula da da lafiyar su da tsaftace muhallin su.

Ya kuma yi kira ga mutane da su harzarta zuwa asibiti a duk lokacin da basu Jin dadin jikin su.

Share.

game da Author