Maryam Sanda ta shirya kasaitacciyar buki kwanaki biyu bayan an bata beli

0

Kwanaki biyu bayan kotu ta ba Maryam Sanda da ake zargin kashe mijin ta Bilyaminu Halliru ta shirya kasaitacciyar bukin cikar shekarar ‘yar ta Alisha shekara daya da haihuwa.

Idan ba a manta ba Maryam ta Sanda dai ta shafe makonni a kurkuku inda ake karar ta da laifin kashe mijinta bayan rashin jituwa da suka samu.

Daily Nigerian da ta ruwaito wannan labari ta ce an dai yi Bukin badde din ne a gidan mahaifiyar ta dake Abuja.

Share.

game da Author