ALLURA ZAI HAKO GARMA: Sanatoci za su yi wa Shehu Sani Zigidir don ya fadi nawa ake biyan su

0

Wasu daga cikin sanatocin da suka zanta da PREMIUM TIMES sun bayyana bacin ran su kan tonan sililin da Sanata Shehu Sani ya yi musu a makon da ya gabata cewa da yi bayan albashin naira 700,000 da suke karba duk wata, akwai miliyan 13.5 da ake basu domin wasu hidimomin su.

Idan ba a manta ba Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani,ya tona wa sanatocin boyayyiyar asirin su da suka dade suna boyewa da ya fadi wa duniya wasu daga cikin kudaden da ake biyan su.

Shehu Sani ya bayyana cewa ko shakka babu kowani Sanata da ke majalisar dattawa a Najeriya na karbar naira miliyan 13.5 duk wata domin gudanar da ayyukan ofishin sa, bayan naira 750,000 ya ke karba a matsayin albashin sa.

Bayan haka kuma ya ce kowani Sanata na da naira miliyan 200 a ajiye domin yi wa mazabar sa ayyuka.

Wannan batu bai yi wa sanatoci da yawa dadi ba inda suka ce hakan da Shehu Sani yayi ya hada su fada ne da mazabun su.

Ko da yake sanatocin da suka zanta da PREMIUM TIMES sun roki a boye sunayen su, saidai cikin kakkausar murya sun tabbatar mana cewa zasu dauki mataki kan Sanata Shehu Sani.

” Lallai zamu dauki mummunar mataki kan Sanata Shehu Sani, domin ya hada mu fada ne da mazabun mu fadi wa duniya abin da ake biyan my duk wata.

” Za mu tabbata shugaban majalisa Bukola Saraki ya hana shi shiga duk wata ganawar sirri da akeyi musamman wanda ake tattauna maganar kudi.

Bayan haka sun kara da cewa zai Iya fuskantar Kwamitin da’a na majalisar domin a hukunta shi.

Da muka nemi ji daga bakin Sanata Shehu Sani, ya ce na zai yi magana kan ‘yan uwan sa ba, amma a saurare shi.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, tun bayan wannan tonon silili da Sanata Sani yayi mutanen Najeriya da dama na ta yi masa tofin Allah ya yi albarka, domin kuwa babu dayan su da ya iya bugun kirji ya fadi wa ‘yan Najeriya hakan.

Share.

game da Author