ZABEN 2019: Za a sake saida katin neman tallafi wa Buhari kuwa?

0

A zaben 2015, dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya nemi taimakon jama’a wajen bukatar gudummawar kudaden kamfen.

Ta haka ne aka rika saida kati, mai kama da katin loda kudi a wayar salula. Jama’a musamman talakawa da matasa sun rika sayen katin, inda kudin kan tafi a cikin asusun tallafa wa Buhari kamfen.

Yanzu kusan shekarar sa uku kenan a kan mulki. A jikin kowane kati an rubuta dalilin da ya sa za ka sayi katin ka tallafa wa Buhari, “mu hada hannu mu ceto Najeriya.”

Wannan kati ya karade fadin kasar nan, lungu-lungu, sako-sako, tsoho da yaro, kowa ya tallafa wa wannan tafiya.

Shin kai da ka sayi ko an hada hannun da kai? An ceto Najeriya din kuwa? Ko za ka sake sayen kati idan an sake sayarwa don zaben 2019?

Share.

game da Author