Har yanzu dai tsugune ba ta kare ba, domin a yau Laraba Majalisar Tarayya suka sake tada batun kudirin sauya rakanun zabe da kuma na Dakarun Zaman Lafiya, wadanda Shugaba Muhammadu Buhari ya ki saw a hannu.
An dawo da kudirin dokokin ne domin su yi musu zaben-raba-gardamar amincewa a zartas da dokar ko da kuwa Buhari bai amince ya sa mata hannu ba.
Sun kuma sake tada batun wasu kudirori da dama wadanda shugaban ya ki sa musu hannu har guda tara.
Dama dai kakakin majalisar tarayyar, Hon. Abdulrazak Namdas, ya bayyana cewa za su yi wa kudirorin karfa-karfa su zama doka, duk kuwa da cewa Buhari ya ki sa musu hannu domin su zama dokoki.
Sai dai kuma an ce a wasu wuraren ba za su yi wa shugaban karfa-karfa ba, saboda akwai wuraren da suka gamsu da dalilin da ya bayar na kin sa wa kudirorin hannu su zama doka.