Mahara sun kashe sojoji 11 a Kaduna

0

A harin bazata da wasu dauke da bindigogi suka kai sansanin sojoji dake Kamfanin Doka a karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna sojoji 11 sun rasa rayukan su sannan wasu uku sun sami raunuka a jikin su.

Harin bai tsaya nan ba har da wasu yan banga basu tsira ba daga maharan.

Wani tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Gwari ne ya tabbatar wa PREMIUM TIMES abin da ya faru sannan ya ce maharan sun far wa sansanin sojin ne a daren Talata da misalin karfe 10:05, a kan babura.

Ya kuma kara da cewa a safiyar Laraban yau maharan sun sake shigowa kauyukan su inda suka ci karo da wasu ‘yan banga a hanyar su ta zuwa kai wa sojoji dauki, daga nan suka yi arangama da su inda mutum tara cikin yan bangan suka sami raunuka.

” A yanzu haka ‘yan bangan suna kwance a asibitin Birnin Gwari.”

A karshe kakakin rundunar ‘One Mechanised Division’ Muhamed Dole yace da zaran sun kammala bincike za su fidda da bayanai a kai.

Sannan shima kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce nan ba da dadewa ba za su bada bayanai kan harin.

Share.

game da Author