SAKO MAKOKO: Kakakin IBB ya maka Sufeto Janar da wasu jaridu kotu

0

Mai bai wa Tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Babangida Shawara a kan hulda da kafafen yada labarai, Kassim Afegbua, ya maka SUfeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya kotu.

Har ila yau, Afegbua na neman kakakin ‘yan sanda Jimoh Moshood da kuma wasu kafafen yada labarai biyu, su biya shi diyyar naira bilyan daya.

Premium Times Hausa ta ga kwafin takardar karar da ya kai a Kotun Tarayya da ke Abuja a yau Talata.

Lauyan Afegbua, Kayode Ajulo ne ya shigar da karar a madadin wanda ya ke karewa.

Kai karar ya biyo bayan sanarwar da jami’an tsaro suka fitar cewa su na cigiyar sa ruwa a jallo, sakamakon takardar da ya fitar wadda a ciki tsohon Shauagaban kasa Bababangida ya ce an gaji da Buhari, ya huta, kada ya fito takarar 2019.

An neme shi ne ganin cewa daga bisani kuma an fitar da wata mai dauke da sa hannun Babangida wadda ya ke karyata takardar Afegbua.

Jim kadan bayan fitar da takardar, sai kuma ga wani jawabi da Babangida ya ce ba shi ya rubuta waccan takarda da Afegbua ya sa wa hannu a madadin sa ba.

Bayan da Afegbua ya tsaya kai da fata cewa da yawun Babbangida ya rubuta takardar, washegari kuma Babangida ya ce da sanin sa aka rubuta takardar.

Wannan katankatana ta jefa kasar nan cikin rudu da waswasi, ganin yadda jawabai biyu daga bakin Babangida suka yi harshen damo.

Kafafen yada labaran da ya maka kotu, sun hada da Gidan Talbijin na NTA na Kasa da kuma Channels.

Afegbua dai ya yanke shawarar garzaya kotu ne, ganin yadda sakon da aka say a aika ke neman zame masa makoko. Ko kuma takardar da aka sa ya rubuta, ta na neman zame masa ‘takardar Multamisu.’

Share.

game da Author