Yadda ake nuna halin ko-in-kula kan kashe-kashen mutane a kauyukan Kaduna na ci min tuwo a kwarya – Shehu Sani

0

Sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, sanata Shehu Sani ya koka kan yadda Fulani da ‘yan ta’adda suka maida kisa ruwan dare a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Ya bayyana hakan ne a zauren majalisar yau Talata inda ya kara da cewa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro sun kasa yin komai akai.

” Karamar hukumar Birnin Gwari ta yi iyaka da jihohin Zamfara, Kebbi da Neja sannan ta na daya daga cikin mazabar da nake wakilta amma sai gashi an wayi gari yanzu garin ya zama ya zama kusan matattaran ‘yan ta’adda shekaru biyu akai.”

” A dalilin zaman dar-dar da mutanen yankin ke fama da shi ya sa masu dan abin hannu suka tattara iyalan su suka koma da zama cikin garin Kaduna,Talakawa cikin su kuwa na nan zaune yunwa na neman ta kar su saboda rashin iya zuwa gonakin su da sauran aiyukansu da suka saba yi ada.”

” Duk wannan kashe kashen da ake yi a jihar Kaduna gwamnati bata ce komai ba sannan gidajen jaridu basa dauka a labaran su ba.”

Ya yi tir da halin ko in kula da gwamnati ta key i kan irin tashi-tsahina da yayi kamari a sassan kasar nan. Sanata Sani ya nuna bacin ran sa game da yadda wadanda ya kamata su fito su nuna rashin jin dadin su karara, sai suna makewa saboda siyasa.

Daga karshe Sani y ace lokaci ya yi da ya kamata a ajiye siyasa a gefe a yi abin da ya kamata. Wanda ya hada da samar wa mutanen Najeriya kariya ta musamman da kuma wadata tsaro a ko-ina a fadin kasar nan.

Share.

game da Author