2019: Buhari ya nada Tinubu ya jagoranci kwamitin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar APC

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya jagoranci kwatimin da zai sasanta rikice-rikice da rashin jituwar da ke neman gurgunta tafiyar jam’iyyar a daidai lokacin da zaben 2019 ke gabatowa.

A cikin wani rubutaccen jawabi da aka fitar ranar Talata, an nada Tinubu ya jagoranci kwamiti mai suna “kwamitin tuntuba, sasantawa da kokarin sake karfafa amincewar juna” a cikin APC.

“Aikin da aka dora wa kwamitin ya hada da raba gardandami, sasanta sabani da rashin jituwa a tsakanin mambobin jam’iyya, shugabannin jam’iyya da kuma a tsakanin masu rike da mukaman siyasa da ke wanzuwa a wasu jihohi da kuma tarayya.”

Sai dai har yanzu Tunubu bai nuna cewa ya amshin tayin jagorancin kwamitin ko bai amsa ba.

Shi kansa Tinubu ya na daya daga cikin masu korafi da gunagunin an maida shi saniyar-ware. Ko da yake dai ya sha nanata cewa shi ba shi da wata matsala da gwamnatin APC ko Shugaba Buhari.

Tun bayan da APC ta kafa gwamnati a cikin 2015 ta afka cikin rikici a jihohi da tarayya baki daya.

Share.

game da Author