NEYMAR: Ga bikin zuwa, zani ya kece!

0

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallonn kafa ta kasar Faransa, PSG, Neymar, ya hadu da matsala, sakamakon raunin da ya ji a lokacin da suke buga wasa da kungiyar Olympic Massille, inda PSG ta yi nasara da ci 3:0.

Wannan ciwo da ya ji bai yi masa dadi ba, daga shi har hukumar gudanarwar kungiyar PSGda sauran masu goyon bayan kungiyar a duniya baki daya.

Dalilin haka shi ne, Neymar ya ji ciwon ne ana saura sati biyu kacal ya buga zagaye na biyu na wasan da kungiyar sa za ta kara da ta Real Madrid da ke Spain, a gasar cin Zakarun Turai, wanda Real din ce ke rike da kofin a shekaru biyu a jere.

An dai tashi wasan farko inda Real Madrid ta caskara PSG a birnin Madrid, da ci 3:1. Kenan sai PSG ta ci kwallaye akalla 3:0 kafin ta yi nasara a kan Madrid.

Kacokan karfin da SPG ke da shi ya dogara ne a kan muhimmiyar gudummawar da suke fatan Neymar zai bayar a wasan na zagaye na biyu, duk kuwa da cewa akwai wasu hazikan ‘yan wasan na PSG, irin su Mpape da Cavani.

A wasan zagaye na farko, Neymar bai yi kokari sosai ba, saboda masu tsaron bayan Madrid, musamman Marcello ya hana shi sakat.

Ciwon da ya ji a wasan su da Olympic ya kawo cikas sosai, domin babu abin da ke gaban PSG sai kokarin cin Kofin Zakarun Turai, da ta ke son karbewa a hannun Madrid.

Kwatsam sai ga shi an ce Neymar zai kwashe sama da wata daya kafin ya dawo buga wasa.

Ana wata kuma sai ga wata, duk da cewa ‘yan wasan OM sun tausaya masa, da yawan su sun bayyana cewa shi ya ja wa kan sa, saboda irin yanayin takun wasan sa, na yadda ya ke rike kwallo ba zai tura wa abokin wasan sa ba.

Sun ce Neymar ya na rike kwallo har sai abokin kafaswar wasa ya kai kafa sannan zai ce ya yi yanka ko kuma sannan zai nemi ya tura wani kwallon.

Sun nuna cewa hakan kan sa idan wani ya kai kafa zai kwace kwallon, maimakon ya same shi, sai ya kafta masa sara a kafa, amma ba da gangan ba.

Gidan talbijin na ESPC ya tabbatar da cewa Neymar na da matsalar rike kwallo, ba ya saurin saki ya tura wa abokin wasan sa. Har ma ESPC ya kawo misalin cewa a wasan PSG da OM, sau takwas ana kayar da Neymar a cikin mintina goma kacal a wurin kokarin a karbi kwallo a hannun sa.

Har ila yau, ESPN ya ruwaito cewa akwai ‘yan wasan OM su uku da suka samu alkalin gefen feli, a lokacin da ana tirka-tirkar wasan, suka yi masa korafin cewa Neymar fa shi ne ke bata wasa, ya na rike kwallo, idan an taba shi kuma sai ya fadi, alkalin wasa ya hura.

ESPN ta tabbatar da cewa a cikin ilahirin ‘yan wasan da ke buga Kofin Zakarun Afrika kafaf na kungiyoyin kasashen Turai, Neymar ne ya fi saurin faduwa, kuma an fi hura usur a lokacin da ya ke rike da kwallo idan wani dan wasa ya shigar masa zai kwace kwallon.

Cikin wadanda suka fi dora wa Neymar laifin abin da ya same shi, har da mai tsaron bayan Olymoic Masislle, Jordan Amani, wanda ya ce ‘‘dama tsuntsun da ya kira ruwa, ai shi rujwa ke duka.’’

Shi kuwa wanda ya ji masa ciwon, har yau bai daina fada da babbar murya cewa shi bai nufe shi da wani mugun nufi ba.

Bouna Sarr, ya jajirce cewa shi fa ya kai kafar sa ne da nufin tare kwallo ko karbe ta daga kafar Neymar kawai. Babu ruwan sa da kafar Neymar. Idan ma ya taka shi, ko ya gwabje shi, to ba da gangan ba.

Amma kuma kaftin na PSG, Tiago Silva, ya ki yarda cda dukkan dalilan da ‘yan wasan Olympic su ka bayar, ya na mai cewa tun da farko dama akwai azazza cewa abokan karawar ta su, sun yi niyyar yin salon kwallon gurugubji da banke-banke.

Ya kuma ce su na sane da gangan su ka rika taka Neymar har suka ji masa ciwo.

Ba wannan ne karo na farko da Neymar ke jin ciwo a wasan kwallo wanda ake tsananin bukatar ya fitar da kungiyar da ya ke ciki kunya ba.

Ko a wasan gasar cin Kofin Duniya da aka gudanar a kasar su Brazil, ciwon da ya ji na daya daga cikin babban dalilin da ya sa kasar Brazil ba ta tabuka abin a zo a gani ba.

Neymar, dan wasan da aka fi saye da tsada a duniyar yau da ta jiya har ma ta shekaranjiya, a yanzu dai ya na jiyyar raunin da ya ji, a daidai lokacin da Real Madrid za ta je maida buki a filin wasan SPG. Sai dai kash, ga biki har biki, amma zanin daurawar Neymar ya kece.

Share.

game da Author