Fadar Shugaba Muhammadu Buhari da iyalan sa sun cika murna, sakamakon dawowar babban dan Shugaban Kasa, Yusuf Buhari, wanda aka dauka zuwa jinya a asibitin Turai, bayan hadarin da yayi a kan babur din tsere.
Jim kadan bayan saukar sa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta nuna matukar godiya da farin ciki ga daukacin ‘yan Najeriya ganin babban dan ta namiji da ke jinya, ya warke kuma ya dawo gida.
A shafin ta na tweeter ne ta yi bayanin a safiyar Alhamis ta na godiya da irin addu’o’in da aka rika yi wa Yusuf har ya warke.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN, ya ruwaito cewa Yusuf ya sauka filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja yau Alhamis da safe.