Yadda sojoji suka ceto wani attajiri a hannu masu garkuwa da mutane a Lokoja

0

Jagoran rundunar ‘Operation Cat Race’ Weri Finikukor ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai cewa sun yi arangama da kungiyar masu garkuwa da mutane a Lokoja inda rundunar ta rasa soja daya sannan suka kashe uku daga cikin masu garkuwan da suka yi arangama dasu.

Finikumor ya ce sun yi wannan batakashi ne ranar 27 ga watan Fabrairu da suke je ceto wani babban mai hada hadan man fetur dake Lokoja mai suna Momoh Otinau dake hannun masu garkuwan.

Shi dai Momoh ya na tsare ne wajen masu garkuwan tun 17 ga watan Fabrairun, wato ranar da aka sace shi a gaban wata masallaci dake Lokoja.

” Bin sawun dan uwan Otinau ne muka yi da ya je biyan kudin da zai fanshi dan uwansa. A nan ne fa muka yi kicibus dasu masu garkun inda koya ya bude wuta. Ana haka ne fa sai Allah ya bamu sa’an kashe uku daga cikin su, sannan muka ceto Otinau.

Share.

game da Author