BOKO HARAM: Kwamitin PCNI da VSF sun tallafawa jihar Barno

0

Kwamitin Shugaban Kasa don raya yankin Arewa Maso Gabas da hadin guiwar gidauniyar ‘Victims Support Fund, VSF’ sun tallafa wa gwamnatin jihar Barno da kayan aikin asibiti da na gini da ya kai Naira biliyan 2.

Jami’in hukumar Alkasim Abdukadi ya sanar da haka wa manema labarai a Maiduguri inda ya kara da cewa hukumar PCNI da gidauniyar VSF sun samar da wannan tallafi ne domin gina gidajen zama a wasu zababbun kananan hukumomi sannan da wadatar su da kiwon lafiya sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar.

Ya kuma ce yanzu haka mataimakin shugaban hukumar PCNI Tijani Tumsa ya damka wadannan kaya ga gwamnan jihar Barno Kashim Shettima ranar Juma’a da ya gabata.

” Za mu raba kayan ginin ne bisa ga yanayin ta’adin da aiyukan Boko Haram ya yi a wadannan zababbun kananan hukumomi da suka hada da Biu, Gwoza, Monguno, Guzamala, Kala-Balge, Kukawa, Mafa, Ngala da Damboa.”

” Bayan haka mun wadata asibitin Bama da na’urar gwaji, gadajen asibiti 240 da sauran su.”

Daga karshe gwamnan jihar Kashim Shettima ya mika godiyar sa ga hukumar PCNI da gidauniyar VSF cewa wannan gudunmuwa abin jinjinawa ne.

Share.

game da Author