Shekau ya kan yi shigar mata don ya Sulale

0

Dakarun Sojojin Najeriya sun bayyana yadda shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi shigar-burtu, ya saka hijabi da nikabi, ya shiga cikin mata ya sulale daga harin dakarun Sojojin Najeriya.

Kakakin Sojojin, Burgediya Janar Sani Usman ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi da ya fitar ga kakafen sadarwa a yau Talata.

Usman ya ce Shekau ya ji uwar-bari, ya kasa daure harin da aka rika kai musu shi da rundunar sa, daga bisani ya yi shigar mata ya sulale, ya gudu ya bar mabiyan sa.

“ Ya gudu ne wai don ya tsira da ran sa, kuma mun ji cewa ya ma rika canja hijabai da nikabi, idan ya sa bakake, can gaba kuma idan ya matsa, sai ya cire ya saka tsanwa. Amma dai ganin karshe da aka yi masa, ya na sanyen da bakin hijabi ne.

“ Don haka mu na sanar da mabiyan sa cewa to sani su na biye da matsoraci ne kawai. Don haka su ajiye makamai su fito su mika wuya. Idan su ka yi haka, babu wanda zai ci zarafin su tunda sun mika wuya ne.” Inji Usman.

Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar jihar Barno, Adamawa da Yobe da su rika yin kaffa-kaffa muddin suka gani ko su ka ji inda Shekau ya lafe, to su sanar da gaggawa.

Share.

game da Author