Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da wata mummunar hadarin mota da aka yi a karamar hukumar Gaya dake jihar inda dalibai 22 suka rasa rayukan su.
Kakakin rundunar Musa Majiya ya bayyana cewa hadarin ta auku ne da misalin karfe 11 na safen Talata inda wata mota kirar Bus ta yi karo da babbar roka.
” Da misalin karfe 11 na safiyar Talata wata mota kirar bus da ta dauko wasu daliban makaranta 22 ta yi karo da wata babbar mota inda daliban nan suka rasa nan take.”
Majiya ya kara da cewa motar wanda ke dauke da daliban wata makaranta daga karamar hukumar Misau jihar Bauchi ta yi hadarin ne a hanyar ta na kai wadannan yara yawon bude ido a gidan wata radiyo a Kano.
Wani wanda hadarin ta faru a idanuwar sa mai suna Tella Mai’Unguwa ya ce sanadiyyar kauce wa wata rami ne dake kan hanyar Dudduru da ke kusa da kwalejin Maitama Sule motar daliban ta yi karo da wannan babbar roka.
Discussion about this post