BOKO HARAM: An ceto wasu daga cikin daliban makarantar Dapchi

0

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da cewa dakarun sojin Najeriya sun ceto wasu daga cikin daliban makarantar Dapchi da ake zargin Boko Haram ta yi garkuwa da su.

Idan ba a manta ranar Litini Boko Haram sun kai wa makarantan mata na Dapchi hari inda suka gudu da wasu Daga cikin daliban.

Ko da yake gwamnatin jihar ta ce adadin yawan daliban da Boko Haram suka sace sun kai 50 amma rundunar ‘yan sandan jihar ta ce 30 ne kawai.

Bayan haka kakakin gwamnan jihar Abdullahi Bego wanda ya bada sanarwa ya bayyana cewa a daren ranar Laraba dakarun sojin Najeriya sun ceto wasu daga cikin daliban makarantar.

” A yanzu haka wadannan dalibai da aka ceto na tare da sojoji.”

Share.

game da Author