Mutane 124 sun kamu da cutar Lassa a Jihar Edo

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa NCDC reshen jihar Edo Osamuwonyi Irowa ya ce sun sami tabbacin cewa mutane 124 sun kamu da cutar zazzabin Lassa daga cikin mutane 521 da ake zargin suna dauke da cutar.

Irowa ya sanar da haka ne a taron kaddamar da sabuwar asibitin kula da masu fama da cutar da gwamnatin jihar ta gina a Benin ranar Laraba sannan ya kara da cewa wadannan mutane sun fito ne daga kananan hukumomi 13 a jihar.

Ya kuma kara da cewa wasu mutane 15 sun rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar sannan wasu 10 sun fara nuna alamun kamuwa da cutar.

” Haka ya sa ma’aikatan kiwon lafiya suka kebe mutane 509 domin tabbatar da cewa basa dauke da cutar.”

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan hukumar NCDC da su hadda hannu da mutane domin karfafa matakan kawar da cutar a jihar.

Ya kuma ce gwamnati na iya kokarinta wajen gina wasu asibitocin kula da wadanda suke fama da cutar Lassa domin rage yawan mutanen dake zuwa asibitin Irrua.

Share.

game da Author